Mun Gama Da ‘Yan Ta’adda Shure-Shure Kawai Suke – Fadar Shugaban Kasa

?aramin Ministan ?wadago Festus Keyamo, ya bayyana cewa kusan yanzu babu sauran ‘yan ta’adda, duk gwamnatin tarayya ta mur?ushe su, “sai ?an ?ur?ushi kawai.”

Ministan ya bayyana hakan ne a cikin wata tattaunawa ta musamman da gidan talabijin na Trust TV ya yi dashi a birnin tarayya Abuja ranar talata.
A shirin tattaunawa da aka yi da Keyamo, gayyaci Daniel Bwala, wanda shi ne Kakakin Kamfen ?in PDP a za?en Shugaban ?asa.

Ya ce labaran da ake watsawa na nuna rashin ?o?arin gwamnatin Buhari da kasa yin wani kata?us a ?angaren tsaro duk ‘yan adawa ne ke ?aukar nauyin buga su a kafafen ya?a labarai.

“Yawan nanata kasawar wannan gwamnatin ya zama tamkar wata wa?a da ‘yan adawa su ka hardace, su ke rerawa a kullum, ba tare da yin la’akari da irin gagarumin ayyukan da wannan gwamnatin ta yi ba.

“Matsalar Boko Haram gadon ta wannan gwamnatin ta yi daga PDP. A lokacin kuwa ?ananan hukumomi 14 na Barno duk a hannun Boko Haram su ke. Wancan lokacin ?ungiyar ?wallo ta El-Kanemi Warriors a Bauchi su ke wasannin su, saboda matsalar tsaro a Maiduguri. Amma yanzu sun koma su na wasan su a Maiduguri.

“Ban ce an kakka?e Boko Haram baki ?aya ba. Amma dai idan aka duba gwamnatin da ta gabata da irin c gaban da wannan gwamnati ta samar, za a san kakka?e su, sai ?ur?ushi su ka rage.

Related posts

Leave a Comment