Ambaliyar Ruwa: Sokoto, Kebbi Borno Na Cikin Hatsari

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Hasashen hukumar kula da yanayi ya nuna cewa za a iya samun ambaliyar ruwa a wasu sassan jihohin Sokoto da Kebbi da Borno da Bayelsa a ‘yan kwanakin da ke tafe.

Shugaban hukumar Farfesa Mansur Matazu ne ya nuna haka a bayanan da ya gabatar a lokacin wani taron manema labarai a Abuja ranar Talata, inda ya ce wasu yankuna a jihohin na fuskantar hadarin ambaliya.

Ya ce nazarin ya nuna musu cewa wadannan jihohi sune suka fi kasancewa cikin hadarin samun mamakon ruwan sama da zai iya haddasa ambaliya.

Ya kara bayani da cewa, “Yankunan da suka fi kasancewa cikin hadarin su ne sassan tsakiyar Borno da sassan arewacin Jihar Kebbi da na Jihar Sokoto.

Hadi da sassan tsakiyar Jihar Kaduna da wasu bangarorin Jihar Bayelsa da Jihar Delta.”

Related posts

Leave a Comment