Kaduna: El Rufa’i Ne Silar Matsalar Tsaro – Shehu Sani

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewa Shehu Sani wanda ya yi Sanata na wa’adi daya a majalisar dattawa, ya zargi Nasir El-Rufai da taimakawa matsalar rashin tsaro a jihar Kaduna.

Shehu Sani ya zanta da gidan talabijin na Arise TV a ranar Lahadi, 14 ga watan Satumba 2022, aka tabo batun wasikar da Gwamnansa ya aikawa shugaban kasa. Sanata Sani yace Gwamna Nasir El-Rufai ya shaidawa Duniya gazawarsa a wannan wasika da ya rubuta zuwa Aso Villa, bayan a baya ya yi ta boye matsalar.

A cewar ‘dan siyasar, a cikin koke-koken da El-Rufai ya yi wa shugaba Muhammadu Buhari, babu wani sabon abin da ba a ankarar da gwamnati tun baya ba. Sani yace a lokacin da ya bijiro da matsalar a majalisa, El-Rufai ya nuna ana zuzuta lamarin, sai ga shi yau ana kukan ‘yan ta’dda na neman kafa gwamnati.

Related posts

Leave a Comment