?aramin Ministan ?wadago Festus Keyamo, ya bayyana cewa kusan yanzu babu sauran yan taadda, duk gwamnatin tarayya ta mur?ushe su, sai ?an ?ur?ushi kawai.
Ministan ya bayyana hakan ne a cikin wata tattaunawa ta musamman da gidan talabijin na Trust TV ya yi dashi a birnin tarayya Abuja ranar talata.
A shirin tattaunawa da aka yi da Keyamo, gayyaci Daniel Bwala, wanda shi ne Kakakin Kamfen ?in PDP a za?en Shugaban ?asa.
Ya ce labaran da ake watsawa na nuna rashin ?o?arin gwamnatin Buhari da kasa yin wani kata?us a ?angaren tsaro duk yan adawa ne ke ?aukar nauyin buga su a kafafen ya?a labarai.
Yawan nanata kasawar wannan gwamnatin ya zama tamkar wata wa?a da yan adawa su ka hardace, su ke rerawa a kullum, ba tare da yin laakari da irin gagarumin ayyukan da wannan gwamnatin ta yi ba.
Matsalar Boko Haram gadon ta wannan gwamnatin ta yi daga PDP. A lokacin kuwa ?ananan hukumomi 14 na Barno duk a hannun Boko Haram su ke. Wancan lokacin ?ungiyar ?wallo ta El-Kanemi Warriors a Bauchi su ke wasannin su, saboda matsalar tsaro a Maiduguri. Amma yanzu sun koma su na wasan su a Maiduguri.
Ban ce an kakka?e Boko Haram baki ?aya ba. Amma dai idan aka duba gwamnatin da ta gabata da irin c gaban da wannan gwamnati ta samar, za a san kakka?e su, sai ?ur?ushi su ka rage.

