Mun Dakile Hari A Kano Da Ka Iya Zama Mafi Muni A Najeriya – Hukumar Tsaro

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Jami’an tsaro sun da?ile wani yun?urin kai hari a Jihar Kano “wanda ka iya zama mafi muni” a tarihin ?asar, a cewar Babban Hafsan Tsaro na Janar Lucky Irabor.

Janar Irabor ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin da ya bayyana cikin wani shiri kan Ranar Dimokura?iyya a kafar talabijin ta Channels TV.

Ya ce an da?ile harin ne a Kano cikin makon da aka kai hari kan wani coci a garin Owo na Jihar Ondo, wanda ‘yan bindiga suka bu?e wa masu ibada wuta tare da kashe mutum fiye da 40.

“Babu mamaki ba ku da labari cewa a makon da ya wuce ka?ai da aka kai harin coci a Owo, a Kano misali, mun yi nasarar da?ile harin da ka iya zama mafi muni a ?asar nan tamu saboda bayanan sirri da muka samu,” in ji shi.

“A wannan aikin, mun gano kayayyakin da ake ha?a abubuwan fashewa da su. Mun ?wace ?unshin makamai masu yawan gaske da miyagu ke ?o?arin yin amfani da su a sassan ?asa, har da Abuja.”

Janar ?in ya ?ara da cewa harin Owo da aka kai ba ya nuna cewa ba a samun ci gaba a fa?in Najeriya ba, yana mai cewa “harkokin tsaro sun inganta a shekara ?aya da ta wuce”.

Related posts

Leave a Comment