Rundunar ‘yan sandan Jihar Ondo ta musanta rahotannin da ke cewa ta kama maharan da suka kashe masu ibada fiye da 40 a harin da suka kai Cocin Katolika na St. Francis a jihar.
Rahotannin da aka dinga ya?awa a shafukan zumunta sun bayyana cewa dakarun ha?in gwiwa na sojoji ne da ‘yan sanda da na rundunar Amotekun suka kama maharan a ranar Alhamis.
Sannan sun yi i?irarin cewa an kai mutanen fadar Mai Martaba Olowo na Owo Oba Ajibade Ogunoye, inda mutane suka yi tururuwa don ganin wa?anda ake zargin.
Sai dai basaraken ya musanta batun kamen yayin hirarsa da jaridar Punch a yau Juma’a. “Rahoton ba gaskiya ba ne,” in ji shi. “Mutane sun yi ta zuwa fada don ganin su amma Olowo ya fa?a musu babu wanda aka kawo fadar.”
