Shugaban Kamfanin ATAR Communication mamallakan gidajen Talabijin da Rediyo na Liberty Alhaji Ahmed Tijjani Ramalan, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su tabbatar sun mallaki katin za?e domin samun nasarar za?ar ‘yan takarar da suka dace a za?en dake tafe na 2023.
Ramalan ya yi wannan kiran ne a sakon murnar ranar dimukuradiyya ta bana 12 ga Watan Yunin Shekarar 2023.
Shugabŕn Kamfanin na ATAR ya bayyana ranar Dimukura?iyya a matsayin wata rana mai muhimmanci a Najeriya sannan ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga ‘yan Nijeriya wa?anda ba su mallaki katin za?e na din-din ba da su yi kokari mallakar katin domin ba su damar za?ar ‘yan takarar da suka dace.
Tijjani Ramalan ya ?ara da cewar tuni gidajen Talabijin da Rediyo na Liberty ya samar da shirye-shirye na musamman ga ‘yan Najeriya domin sanin cigaban da ake samu a mulkin dimukuradiyya da wayar musu da kai akan muhimmancin mallakar katin za?e ta hanyar ha?in gwiwa tsakanin ‘yan siyasa da Jam’iyyu.
Daga karshe shugaban Kamfanin ya bukaci ‘yan Najeriya da dagewa wajen sanya ?asa cikin addu’o’i domin samun zaman lafiya da cigaban ?asa gaba daya.
