Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna damuwarsa kan halin rashin tsaro da ?asar ke fama dashi, yana mai cewa “abin na damun sa a kullum”.
Cikin jawabinsa na Ranar Dimokura?iyya a ranar Lahadi, Buhari ya ce shi da jami’an tsaro na yin iya bakin ?o?arinsu don ganin an sako duk wa?anda aka yi garkuwa da su.
“A wannan rana ta musamman, ina so mu saka dukkan wa?anda hare-haren ‘yan ta’adda ya shafa cikin addu’o’in mu”.
“Ina kwana ina tashi kullum da ba?in cikin duka wa?anda aka sace da kuma wa?anda hare-haren ‘yan ta’adda ya shafa. Ni da jami’an tsaro muna yin dukkan mai yiwuwa don ganin an sako mutanen maza da mata cikin ruwan sanyi.
“Wa?anda suka rasa rayukansu, za mu ci gaba da nema wa iyalansu adalci a kan miyagun.
