Shugaba Muhammadu Buhari ya jaddada halin sa da ya da?e ya na nunawa, inda wannan karo ma ya ce ayyukan da gwamnatin sa ta yi wa Najeriya sun zarce na dukkan shugabannin da aka yi tun daga 1999 zuwa yau.
Buhari na magana ce a kan gwamnatocin Obasanjo, Umaru ‘Yar’Adua da Goodluck Jonathan.
Ya yi wannan i?irari ne a cikin jawabin sa na murnar cikar Najeriya 61 da samun ‘yanci a ranar Juma’a.
Sai dai kuma sahihan hujjojin ayyukan da aka yi a ?asa sun nuna babu ?amshin gaskiya a jawabin na Buhari.
“Babu gwamnatin da ta yi aikin da mu ka yi a cikin shekaru shida tun daga 1999 zuwa yau.” Haka ya furta a cikin jawabin.
Duk Da Buhari Ya Yi Bajinta A Wasu Fannoni, Akwai Inda Bai Ta?uka Ba:
Gwamnatin Buhari ba ta ta?uka ba fannin inganta tattalin arziki, fannin tsaro, fannin inganta ilmi da kiwon lafiya.
Haka kuma a fannin ya?i da cin hanci da rashawa, babu wani ?o?arin da gwamnatin Buhari ta yi fiye da na gwamnatocin Obasanjo, Umaru da Goodluck Jonathan.
Matalauta da masu fama da ?uncin rayuwa sun fi yawa a yanzu fiye da shekarun baya kafin Buhari ya hau a 2015.
Sannan gwamnatin sa ta shiga ruguguwar rashin iya ayyuka da almubazzarantar da dukiya.
Haka a ?angaren adawa, yayin da aka kafa APC a kan mayafin bajau ?in adawa, bayan Buhari ya hau mulki sai gwamnatin sa ta fi ta Obasanjo da Umaru da Jonathan ya?i da nasu adawa da gwamnati.
Tsadar Kayan Abinci Lokacin Da Gwamnati Ke Barka Ku?i A Fannin Noma:
Duk cewa a kullum talakawa na jin labarin irin ma?udan ku?a?en da gwamnati ke narkarwa a fannin bun?asa noma, tsadar abinci sai ci gaba ta ke yi da kassara masu ?aramin ?arfi a ?asar nan.
Kusan farashin komai na abinci ya nunka daga hawan Buhari a 2015 zuwa yau.
Miliyoyin jama’a na zargin cewa ku?a?en da ake warewa domin bun?asa noma, ba su zuwa hannun wa?anda ake ware ku?a?en don su. Kuma har yau ba a kama ko mutum ?aya da laifi ba.
Matsalar Tsaro: Shugaban da aka za?a saboda ya na ta bugun ?irji da kirarin zai iya magance matsalar tsaro cikin ?an?anen lakaci, sai ga shi jihar sa ta afka cikin mummunan halin da ba ta ta?a samun kan ta ba a tarihin kafuwar Najeriya.
A kan idon sa ‘yan bindiga sun kafa ‘dauloli’ a Katsina, Zamfara, Sokoto, Neja, Kaduna da wasu sassa.
Har yanzu Boko Haram na cin kasuwa a Arewa maso Gabas. Kuma shirin gwamnatin sa na yafe wa ‘yan ta’adda ana ba su jarin kama sana’a, kusan abu ne da akasarin ‘yan Najeriya ba su yi murna da shi ba.
A ?ar?ashin mulkin Buhari kusan babu jihar da ba a cikin tashin hankali a ?asar nan, sai wasu ‘yan tsiraru.
A lissafin munin ta’addanci a duniya, Najeriya ce ?asa ta uku, a lissafin da aka yi na cikin 2017.
A ?ar?ashin gwamnantin Buhari ‘yan tada ?ayar baya masu neman ?allewa a Najeriya sun ?ara bayyana sosai. Kuma ?abilanci da ?angaranci ya ?ara ruruwa.
A ?angaren cinikayya a ?asashen waje kuwa, yawancin farashin kaya a ?asashen ?etare bai canja ba tun daga 2015 zuwa yau. Amma kayan da ka sayo a dala miliyan 1 shekaru hu?u baya, idan Naira miliyan 200 ka canji dala, to a yanzu sai ka canje ta fiye da Naira miliyan 400.
Wannan shi ne irin ci gaban da aka samu daga 2015 zuwa yau.
