A yayinda aka gudanar da bikin ranan samun yancin kai a Najeriya wanda ta cika shekaru sittin da samun yanci daga turawan ingila
a shekara ta 1960.
An baiyana cewa tun daga wancan lokacin zuwa yanzu an samu cigaba a bangarori daban daban da suka hada da gine gine ilimi da dai sauransu.
Alhaji Adamu Jingi wanda akafi sani da mai hange kuma ahugaban makarantar NAFAN ACADEMY ne ya baiyana haka a zantawarsa da muryar yanci dangane da cika Najeriya shekaru sittin da daya da samun yancin kai a yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.
Alhaji Adamu Jingi yace kawo yanzu an samun cigaba duk da cewa kasar na fuskantar matsakar tsaro a sassa daban daban a fadin Najeriya wanda suka hada dana boko haram, yan bindiga, yan fashi da makami da dai sauransu.
Don haka nema ya kirayi gwamnatin tarayya dana jihohi da suyi dukkannin maiyiwa domin ganin an kawo kashen matsalar tsaro baki daya.
A bangaren ilimi kuwa ya kirayi yan kasuwa da su shiga a dama da su wajen bunkasa ilimi a fadin kasar ta Najeriya wanda a cewarsa samar da wadaceccen ilimi zaitaimaka wajen wanzar da zaman lafiya mai daurewa a fadin Najeriyar baki daya.
Haka kazalika a shashin tsaroma ya kirayi yan Najeriya tare da Jami an tsaro yan sa kai irinsu yan banga, mafarauta da dai sauransu da su kasance masu baiwa hukumomin tsaro hadin kai da goyon baya domin ganin an kai ga kawo karshen matsalr baki daya.
Alhaji Adamu ya kuma ahawarci gwamnatin da ta sake damtse wajen koyawa daluben makarantu sana o i daban daban da suka hada da kiwo, noma, yin kere kere, da dai sauransu.
Ya kuma kirayi sarakunan gargajiya da malamai shuwagabanin addinai da suma suna da muhimmiyar rawa da zasu iya takawa wajen hadin kan kasa harma da samar da zaman lafiya a tsakanin al umma bakai daya.
SheYa kuma taya yan Najeriya murnan bikin ranan samun yancin kai tere da kiransu da su cigaba dayin adu o i a koda yaushe domin ganin an samu zaman lafiya dama cigaban kasanan baki daya.
