Rundunar Soji Ta Banka Wa Jirgin Ruwan Satar Danyen Mai Wuta

Rahotanni daga yankin Naija-Delta na bayyana cewa Jami’an tsaron Soji sun cinna wa jirgin ruwan dakon mai da aka kama ?auke da ?anyen mai na sata wuta a yankin Escravos na Naija-Delta.

Wannan ne irin haka na biyu a cikin wata tara.

A ranar Litinin ne kamfanin man fetur na ?asa NNPCL ya sanar da kama jirgin ruwan ma?are da ?anyen man fetur.

Hukumomi sun ce jirgin wanda ke kan hanyarsa zuwa ?asar Kamaru, na ?auke da ?anyen mai lita 800,000, wanda ya sato daga wani yanki na jihar Ondo a kudancin Najeriya.

Jirgin, mallakin wani kamfani na Najeriya, hukumomi sun ce ya kwashe shekara 12 yana aiki cikin sirri.

Sai dai babu tabbaci ko an kwashe ?anyen man kafin cinna masa wuta ko a’a.

?angaren man fetur na Najeriya ya kwashe shekaru yana fama da rashawa da satar ?anyen mai da kuma kafa matatun man fetur ba bisa ?a’ida ba.

A shekarar 2022 gwamnatin Najeriya ta ce tana asarar sama da gangar mai lita 470,000 a kowace rana sanadiyyar ayyukan ma?arnata.

Gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta sha alwashin ya?i da satar ?anyen man fetur, wanda shi ne babbar hanyar samun ku?a?en shiga na ?asar.

Related posts

Leave a Comment