Labarin dake shigo mana daga birnin Ikko na jihar Legas na bayyana cewa Yemi Farounbi, tsohon Jakadan Najeriya a kasar Philippine, yace Shugaban kasa Muhammadu Buhari ladabtarwar ce daga Ubangiji da ake yi wa ‘yan Najeriya.
Farounbi ya sanar da hakan ne a ranar Asabar yayin da aka tattauna da shi a shirin gidan rediyo a Ayekooto a Splash 105.5FM. Yace an ja kunnen ‘yan Najeriya kan tarihin Buhari da kuma yadda ya garkame ‘yan siyasa masu tarin yawa amma suka yi kememe.
“A 2014 zuwa 2015 lokacin da ‘yan Najeriya suka yanke shawarar karbar kamfen din, an ja musu kunne kan tarihin shugaban kasa Muhammadu Buhari da yadda ya garkame ‘yan siyasa da suka hada da Chif Obafemi Awolowo, da sauran manya daga sassan ?asar”.
“Ubangiji yana da abin mamaki. Ya yanke shawarar yin amfani da Buhari wurin ladabtar da shaidancin ‘yan Najeriya, kuma ‘yan Najeriya sun cancanci ladatarwa. “Najeriya ba yadda ake tsammani take ba. Ina da tabbacin Najeriya zata cigaba.
