Rijistar Katin Zabe: An Yi Barazanar Maka INEC Kotu

?ungiyar SERAP mai fafutukar ya?i da cin hanci ta bu?aci shugaban hukumar zabe ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya tsawaita wa’adin rajistar katin za?e ko ta maka shi kotu.

?ungiyar ta yi wannan kira ne a wata wasika da mataimakin shugabanta, Kolawole Oluwadare ya fitar a ranar Asabar.

Kungiyar ta bukaci INEC ala tilas ta ba ‘yan Najeriya miliyan 7 da suka yi rajista a intanet damar kamala cike ka’idar mallakar katin.

INEC ta bayyana cewa cikin ‘yan Najeriya 10,487,972 da suka yi rajistar katin zabe ta intanet, mutum 3,444,378 ne kawai suka samu damar karban katinsu.

Serap ta ce akwai bukatar ayi wa mutane uzuri la’akari da kalubalen da ‘yan Najeriya ke fuskanta a cibiyoyin karban kati a sassan Najeriya.

Related posts

Leave a Comment