Rahotannin dake shigo mana daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kamfanin bincike kan harkokin tsaro a yankin Sahel na Beacon Consulting ya ce yawan hare-haren da ‘yan bindiga ke kaiwa a Najeriya ya karu a watan jiya na Yuli da kashi 35 idan aka kwatanta da wanda ya gabace shi.
A cikin wani rahoton da ya fitar a ranar Litinin kamfanin ya ce an kai hare-hare har sau 506 A kananan hukumomin kasar 236.
Hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutum 576 da kuma sace wasu mutum 525.
Sai dai rahoton ya nuna yawan mace-mace sakamakon hari ya ragu da kashi 24 cikin ?ari a watan Yulin.
Yayin da satar jama’a ta ragu da kashi 19 cikin dari idan aka kwatanta da watan ya gabace shi na Yuni.
A tattaunawarsa da BBC shugaban kamfanin Dr. Kabir Adamu ya ce watan Yuli ya kasance mafi sarkakiya ta fuskar tasaro a tarihin Najeriya na nan kusa-kusa, inda aka yi taron majalisar tsaro har uku a dalilin yanayi na tayar da hankali.
Ya ce babban abin da ya tayar da hankalin shi ne harin da aka kai gidan yarin Kuje a karkashin Babban Birnin Tarayya Abuja, wanda hakan ya sa fargaba kan za a iya kai wa birnin da ma wasu jihohi na kusa hari.
Dr Kabiru ya kara da cewa bayan harin sai kuma ya kasance jami’an gwamnati da suka kai ziyarar duba abin da ya faru a gidan yarin sai suka rika bayar da bayanai masu karo da juna.
Hakazalika ofisoshin jakadanci a Abujar sun fitar da gargadi ga ‘yan kasashensu a kan su yi taka tsan-tsan a kan halin da ake ciki a kasar, wanda wannan duk ya nuna irin mawuyacin halin da kasar ta shiga a harkar tsaro a wannan lokaci.
Ta?ar?arewar tsaro na ?ara ?azancewa a ?asar a cikin ‘yan watannin nan, inda rahotannin suka bayyana cewa shugaban ?asa Buhari ya bada umarnin shafe ‘yan ta’adda har sau 29 amma kwalliya ba ta biya ku?in Sabulu ba.
Kungiyoyin daban daban a kasar na cigaba da tsokaci dangane da halin da kasar ke ciki, inda wasu kungiyoyin ke kira ga shugaban da ya yi gaggawar korar shugabannin tsaron kasar, yayin da wasu ke kira ga shugaban da ya kori mai bashi shawara kan harkokin tsaro Janar Monguno mai ritaya.
