Shugabancin APC: Yadda Gwamnoni Suka Yi Wa Mala Buni Juyin Mulki

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Jam’iyyar APC mai mulki ta afka cikin ru?ani bayan gwamnan Neja Abubakar Bello ya rantsar da sabbin shugabannin jam’iyyar na jihohi a Abuja a matsayinsa na sabon shugaba.

Gwamnan jihar Neja Bello ne ya jagoranci jam’iyyar a madadin Mala Buni da shine ke shugabancin jam’iyyar tun bayan da jam’iyar ta yi sallama da Adams Oshiomhole a 2020.

An ruwaito cewa wasu gwamnoni da suka ha?a da na Kaduna, Jigawa, Ekiti, Filato,Neja sun garzaya wurin shugaban Kasa Muhammadu Buhari inda suka kai masa kukan yadda Mala Buni ke kitsa tuggun rugurguza za?en jam’iyyar ta Kasa wanda za a yi a karshen watan Maris.

Wani gwamna daga kudu ya bayyana cewa a gaban sa shugaba Buhari a wajen wannan taro ya bada umarnin a musanya Buni da Bello sabo da matsalolin da ya jefa jam’iyyar a ciki

Da yake tattaunawa da ?an jarida a ofishin jam’iyyar a Abuja bayan rantsar da shugabannin jam’iyyar na jihohi da yayi, gwamna Bello ya ce ya rantsar da su ne a madadin gwamna Buni da bashi kasar yanzu haka.

Related posts

Leave a Comment