Miliyan 100: A Binciki Duk Wanda Ya Sayi Fom Din APC – PDP

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta bukaci hukumomin tsaro musamman masu yaki da cin hanci da rashawa da su kaddamar da bincike kan dukkan ‘yan takarar da suka biya Naira miliyan 100 ko Naira miliyan 50 domin sayen fom din tsayawa takara.

Jam’iyyar ta ce ya dace a binciki inda suka samo kudaden.

Cikin wata sanarwa, PDP ta ce, “Wannan abu ne mai daure kai kuma na rashin nuna tausayi matuka. Lallai ya dace a binciki wadanda ke sayen fom din tsayawa takara kan Naira miliyan 100 da Naira miliyan 50, kan tuhumar sun aikata zamba.”

Related posts

Leave a Comment