Labarin dake shigo mana daga Ibadan babban birnin jihar Oyo na bayyana cewa Allah ya yiwa Sarkin Oyo, babbar Sarki a kasar Yarbawa, Oba Lamidi Adeyemi, rasuwa.
Oba Adeyemi ya mutu ne da yammacin Juma’a a Asibitin koyarwa na jami’ar Afe Babalola dake Ado Ekiti.
Cikin dare aka gaggauta kai gawarsa fadarsa dake birnin Oyo domin fara shirin jana’izarsa.
Adeyemi ya mutu yana mai shekaru 83 bayan kwashe shekaru 52 kan mulki.
