A tattaunawarsa da BBC, Gwamna Wike na jihar Ribas ya ce ba zai yi masalaha da kowanne mutum da ke neman jam’iyyarsu ta PDP ta tsayar da shi takara a zaben na 2023 ba.
“Daya daga cikin abubuwan da suka sa nake neman shugabancin Najeriya shi ne, kamar yadda kuke gani, kasar nan tana cikin matsala, kuma kowa yana kokawa. Ana kashe mutane ko wacce rana, talauci ya yi wa jama’a katutu.
Hakan ne ya sa na yi tunanin shiga takarar shugabancin Najeriya. Ina da kwarewa domin kuwa na yi shugabancin karamar hukuma na shekara shida, na yi minista kusan shekara hudu kuma na zama gwamna”.
