Matsalar Tsaro: ‘Yan Majalisa Sun Yi Yunkurin Tsige Buhari

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Sanatocin jam’iyyun adawa sun fice daga zauren majalisar dattawan a fusace, bayan da aka yi watsi da kudurin da suka gabatar na tsige Shugaba Buhari.

An ruwaito cewa ‘yan majalisar na jam’iyyun adawa sun ba shugaban kasar Muhammadu Buhari wa’adin makwanni shida da ya kawo karshen matsalar tsaro da kasar ke fama da ita.

Sun kuma yi barazanar fara batun tsige shugaban matukar ya kasa magance matsalar cikin wa’adin da suka ba shi.

Shugaban marasa rinjaye na majalaisar, Sanata Phillip Aduda ne ya gabatar da ?udirin a gaban zauren majalisar, inda ya roki shugaban majalisar Ahmed Lawan da ya amince majalisar ta tattauna batun tsaro, da kuma na tsige shugaban kasar.

To amma shugaban majalisar dattawan ya ?i amincewa da bukatar dan majalisar yana mai cewa sam-sam ?udirin bai dace ba.

Related posts

Leave a Comment