Kotun tarayya da ke zamanta a Kano, ta ?i amincewa da bu?atar mayar da shari’ar Sheikh Abduljabbar Kabara zuwa babban birnin tarayya Abuja.
Abduljabbar dai ya bukaci kotun da ta mayar da shari’ar tasa zuwa Abuja saboda zargin da yake na cewar kotun Kano ba za ta yi masa adalci ba.
A zaman kotun na ranar Laraba ?ar?ashin Mai Shari’a Abdullahi Liman, lauyan Abduljabbar Barista Dalhatu Shehu Usman ya zargi alkalin kotun ta Kano da ganawa da kwamsihinan shari’a Barista Musa Lawan a safiyar ranar gabanin zaman kotun.
Sai dai a martani da lauyan gwamnati Barista Dahiru Muhammad ya yi ya ?alubalanci wannan batu, inda ya sanar da kotun cewar tun karfe 9 na safiya masu gabatar da ?arar suka ba shi kwafin sabuwar ?arar da suka shigar a Abuja na zargin take masa hakkinsa.
Daga nan sai Mai Shari’a Abdullahi Liman ya ce ba zai rufe shari’ar ba, sannan a shari’ance babu inda aka ce ?angare daya da ake shari’a da shi zai ce lallai shi ga kotun da yake bu?ata da ta saurari shari’ar.
