Yajin Aikin ASUU: Kungiyar Kwadago Reshen Adamawa Ta Bi Sahun Zanga-Zanga

Kungiyar kwadago a jihar Adamawa ta bi sahun takwarorinta na jhohi wajen yin zanga-zangar lumana a wani mataki na matsawa gwamnatin tarayya lamba domin ganin an kawo karshen yajin aikin da kungiyar malaman Jami’o’i wato ASUU keyi a fadin Najeriya.

Zanga zangar wanda aka fara daga sakatariyar kungiyar dake birnin Yola aka kuma kitseshi a kofar gidan gwamnatin jihar ta Adamawa.

Kwamured Emanuel Fashe shine shugaban kungiyar kwadagon a jihar Adamawa ya bayyana cewa sun dauki matakin hakane domin shaidawa gwamnatin damuwarsu na rashin kawo karshen takaddamar dake tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar ASUU.

Saboda haka ne suka fito wannan zanga zangan lumana domin marawa takwararsu ta ASUU baya wanda kuma aka gudanar a fadin Najeriya.

Da yake nashi jawabi gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri wanda shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar Sunday Edga ya wakilta ya tabbatar musu da cewa zai isar ta sakonsu ga Gwamna domin isarwa ga gwamnatin tarayya.

Shima a jawabinsa shugaban kungiyar Malaman Jami’o’i shiyyar Jami’ar Modibbo Adama dake Yola yabawa yayiwa kungiyar kwadagon bisa goyon baya da suka basu na ganin cewa gwamnatin ta biya musu bukatunsu.

Shi kuwa kakakin rundunan ‘yan sandan jihar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje yace sun dauki matakin ganin cewa zanga zangar ta gudana cikin kwanciyar hankali ba tare da anci zarafin wasu ba.

Zanga zangar dai ta gudanane cikin rakiyar Jami’an ‘yan sanda da dama Wanda Kwamishinan ‘Yan sandan jihar Adamawa Sikiru Kayode Akande ya tura domin ganin komai ya tafi daidai.

Related posts

Leave a Comment