Shugaban Dakarun Soji Ya Kammala Rangadi A Katsina

Rahotanni daga Jihar Katsina na bayyana cewar Babban hafsan Sojojin kasa (COAS), Faruk Yahaya, ya umarci sojojin Najeriya da su kai farmaki zuwa maboyar ‘yan ta’adda da’ yan fashin daji dake addabar jama’a a yankin Arewa maso yammacin kasa.

Kwamandan rundunar ya bayar da umarnin a ranar Juma’a, 7 ga watan Agusta, lokacin da yake yi wa sojoji jawabi a sansanin Fort Muhammadu Buhari dake Daura ta jihar Katsina.

Yahaya ya bayyana cewa duk da cewar akwai ?alubale, amma yakamata sojoji su ?uduri aniyar cin nasarar ya?in, domin karasa ragowar ‘yan ta’addan da suka saura.

“Wannan shine abin da muke yi kuma wannan shine abin da za mu ci gaba da yi. Domin duk wurin da na wuce, sakona kenan. Dole ne mu kai ya?in zuwa wuraren abokan gaba a nan arewa maso yamma har ma a arewa maso gabas inda muke gudanar da su.”

Related posts

Leave a Comment