Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana galibin jama’ar jihar sun bayyana cewa sun dawo daga rakiyar Gwamnati kan matsalar tsaro inda suka ce sun rungumi Addu’a, kawai a Masallatai da Majami’u.
Hakan na zuwane bayan yadda ‘yan Bindiga ke cigaba da cin karensu babu babbaka a jihar, tun daga satar ?alibai da talakawa lamirin yanzu ya kai har ana satar Sarakuna iyayen al’umma a jihar, kuma babu katabus daga ?angaren gwamnatin jihar ?arkashin jagorancin Nasiru El Rufa’i.
Wasu daga cikin jama’ar Jihar da aka zanta su sun bayyana yanke tsammanin su daga gwamnatin, wadda suka bayyana a matsayin wadda ta gaza wajen sauke nauyin samar da tsaro a Jihar.
Wata daga cikin iyayen daliban Bethel Baptist da ‘yan Bindiga suka sace a jihar Madam Esther Joseph ta bayyana cewa, har yanzu diyarta bata dawo daidai ba tun bayan da aka sako ta daga hannun ‘yan Bindigar.
Tace diyar tata tana rika yin sambatu. Ta kara da cewa sai da ta biya Naira 500,000 kudin fansa sannan aka sako mata diyarta, amma hukumomi sun bayyana cewa ba’a biya kudin fansa wajan sako dalibanba.
Da yawan iyayen daliban sun koma Addu’a maimakon dogaro da gwamnati ta dawo musu da ‘ya’yansu, domin a fili yake gwamnatin ta gaza.
