ALLAHU Akbar! Masu iya magana su ka ce rai ba?on duniya. Wannan batu haka ya ke.
A safiyar ranar Alhamis, 6 ga Mayu, 2021 Allah ya yi wa jaruma Khadija Abubakar Mahmud rasuwa.
Khadija ta rasu a garin Jalingo, babban birnin Jihar Taraba, da misalin ?arfe 6 na safe a hannun mahaifiyar ta a kan hanyar su na zuwa asibiti.
Cikin alhini, mahaifiyar ta shaida wa mujallar Fim cewa sun ?auki Khadija sun kai ta wani asibitin ku?i, amma da zuwan su likitocin asibitin su ka ga halin da ta ke ciki sai su ka tura su Federal Medical Centre.
A kan hanyar su ta zuwa asibitin da aka tura su ne Allah ya ?auki ran jarumar.
Marigayiyar ta rasu ta na da shekara 35 a duniya.
Khadija ta ?auki tsawon shekara ?aya ta na gama da rashin lafiya. Ta yi fama da wani irin ciwo ne wanda ke ?one jinin jikin ta wanda ke sawa jini ko leda nawa aka saka mata lokaci ka?an zai ?one.
A haka dai ta samu lafiya na wasu lokuta, sannan kuma ciwon ya dawo.
Allah ya ji?an ta da rahama, ya sa ?arshen wahalar kenan, amin.
Ka?an daga cikin finafinan da ta fito a ciki sun ha?a da ‘Rikicin Duniya’, ‘Uwar Miji Ko Kishiya’, da kuma ‘Uwar Miji Na’.
Daga Mujallar Fim
