Gwamnatin Kano Ta Kai Agaji Ga Iyalan Wadanda Ambaliyar Ruwa Ya Ci

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Gwamnatin jihar ?arkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta bada tallafin kudi dubu N200,000 ga kowanne ?aya daga cikin iyalan mutum 18 da ambaliyar ruwa ta kashe a Doguwa.

Gwamnan ya kai ziyara ta musamman domin ta’aziyya ga iyalan mamatan ranar Lahadi. Ya kuma yi addu’ar samun rahama ga wa?anda suka rasu sanadiyyar ruwan sama mai tsanani, wanda ya haifar da ambaliya.

“Lokacin da labarin ya iso garemu mun ka?u sosai, muna addu’a Allah ya gafartawa wa?anda ruwan ya tafi da rayuwarsu.” “Muna musu Addu’a Allah SWT ya sanya su a cikin rahamarsa ta aljannatul Firdausi, Ameen”.

Wa?anda lamarin ya shafa sun fito ne daga garin Doguwa, ?aramar hukumar Doguwa, mai nisan kilomita 200 daga cikin kwaryar birnin Kano.

Gwamna Ganduje yaje ta’aziyyar ne tare da shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan Najeriya, Alhassan Ado Doguwa. Sauran sun ha?a da shugabannin jam’iyyar APC na jihar Kano, kwamishinoni da kuma wasu mambobin majalisar zartarwar jihar.

Iyalan wa?anda abun ya shafa sun nuna matukar farin cikin su tare da godiya ga gwamna Ganduje bisa nuna kulawarsa. Hakazalika sun yiwa gwamnan fatan Alkairi tare da addu’ar Allah ya ba shi ikon sauke nauyin da aka ?ora masa.

Related posts

Leave a Comment