Wani rikcin ?abilanci tsakanin Fulani da Irigwe da ya ?arke a Jihar Filato da ke arewacin Najeriya ya yi sanadiyar mutuwar mutum hudu a karamar hukumar Bassa da ke Jihar.
Kakakin ‘yan sanda na jihar ASP Ubah Gabriel ya tabbatar wa da Jahidar Daily Trust ce wa an kona gidaje kimanin 50 yayin rikicin.Quote Message: A ranar 31 ga watan Yulin jiya ne, muka samu rahoton barkewar rikici tsakanin wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne da matasan Irigwe a Jebbo Miango da ke Bassa, kuma abin takaici an kona gidaje 50 an kuma harbe mutum hudu … in ji ASP Ubah Gabriel
A ranar 31 ga watan Yulin jiya ne, muka samu rahoton barkewar rikici tsakanin wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne da matasan Irigwe a Jebbo Miango da ke Bassa, kuma abin takaici an kona gidaje 50 an kuma harbe mutum hudu … in ji ASP Ubah Gabriel
“Bayan karbar rahoton, aka aike da dakaru na musamman domin tabbatar da tsaro a yankin da kuma tabbatar da doka da oda.
“Kwamishinan yan sanda Edward Egbuka, da wasu manyan jami’ai sun ziyarci inda lamarin ya faru tare da umarnin gudanar da binciken gaggawa kan gano musabbabin wannan rikici.
“Amma yanzu komai ya koma daidai a yankin,” in ji shi.
