Masu Hankoron Neman Shugabancin Najeriya Su Hakura Tinubu Sai Ya Shekara Takwas – Ganduje

images 2024 03 06T195109.222

Shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa shugaban Kasa Bola Tinubu zai ci gaba da zama shugaban Najeriya har bayan 2027.

Ganduje ya bayyana haka a lokacin da ya ke jawabi ga dandazon magoya bayan Jam’iyyar APC a sakatariyar Jam’iyyar da ke Abuja.

Ganduje ya ?ara da cewa tun ba a kai ko ina ba jam’iyyun adawa sun fara kerma tsoron yin gaba da gaba da APC a zabuka masu zuwa bayan ?an karan kayin da suka sha a za?en 2923.

” Jam’iyyar NNPP sun fi duk jam’iyyun Ki?imewa. Sai tsalle-tsalle suke yi ba su nan ba su can. Kuma wai fa duk shirin 2027 su ke yi.

” Abinda zan fa?i musu kuwa shine kujerar shugaban kasa ta Tinubu, ba a bu?atar canja ta. Saboda tun yanzu sun sha kasa. Kuma ku sani cewa muna sane da wa?anda ke kokarin kawo ru?ani a jam’iyyar mu, kawai don a rika cewa an samu ?araka.

” Su sani muna nan tm?aure tamau kamar yadda aka san mu, ba bu abinda ya girgiza ko yake bamu tsoro. Su je can su cigaba da kulla makircin su mu kuma nuna nan muna kara shiri.

” Idan da za ku yi nazarin yadda abubuwa ke faruwa a jihar Kano za ku ga cewa ko su kansu jam’iyyar Adawa a rabe suke.

Related posts

Leave a Comment