An fara shiga matsalar tsadar man fetur ne tun daga ranar 29 ga Mayu, 2023, ranar da aka rantsar da Shugaba Bola Tinubu, inda tun a kan mimbarin rantsuwa ya bayyana cire tallafin fetur, wanda nan take sai da ya dangana lita ?aya ta kai 650 a cikin sati ?aya.
Tun daga nan kuma tsadar rayuwa ta ri?a kwankwatsar marasa galihu, talakawa da masu ?aramin ?arfi.
A Kano, yawancin masu motoci duk sun ajiye, wasu motocin kuma duk su na kan layin mai, ana jiran tsammani, amma kuma farashin a ranar Litinin ?in nan ya ma haura Naira 1,000.
Wakilin mu ya shiga harabar katafaren Masallacin Bilal da ke unguwar Karkasara, inda ya ga motoci jingim a cikin harabar da rana.
Yawancin motocin na ma?wautan Masallacin ne, wa?anda ke ajiye su a cikin harabar da dare, su na kwana a harabar, wata?ila saboda ?arancin wurin ajiye motoci a gidajen su.
To sai dai kuma wakilin mu ya lura kusan kashi 85% bisa 100% na motocin ba a fita da su ba, saboda ?arancin fetur da kuma tsadar sa.
Dukkan gidajen mai da ake sayar da fetur a Kano, akwai dogayen layukan motoci da babura. Sannan kuma ga tsananin zafin rana, wadda ke fara ku?a tun daga ?arfe 10:30 na safiya.
Yadda ake fama da ?arancin fetur a Kano, haka lamarin ya ke a Jigawa da Babban Birnin Tarayya, Abuja.
