Wata kotun tarayya da ke a Kaduna ta ci tarar ‘yan sanda Naira miliyan 300 kan ‘yan Shi’a uku da aka yi zargin jami’an sun kashe a Zariya a shekarar 2022.
Kotun wacce ta yanke hukuncin bisa la’akari da sashe na 33, 38, 40, 42 da 46 na kundin mulkin ?asar na 1999, ta ce za a biya iyayen yaran da aka kashe kudaden.
Kotun ta kuma yi amfani da doka ta 2, mai hukunci na 1, 2, 3, 4, 11 da 12 a dokar ‘yancin dan Adam (tabbatar da bin dokar) a wajen yanke hukuncin. Baya ga wannan, kotun ta ce ta kuma yi amfani da doka ta 2009; bayani na 4, 8, 10, 11 da 12 da ke a dokar ‘yancin al’ummar Afrika da aka yi a 2004.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito alkaliyar kotun, Hauwa Buhari ta ce za a biya Naira miliyan 100 ga iyayen kowanne yaro da aka kashe.
Haka zalika ta umarci rundunar ‘yan sandan da ta rika biyan kaso 10 na wadannan kudi a matsayin kudin ruwa duk shekara har zuwa ta biya kudin gaba daya.
Mai Shari’a Hauwa Buhari, ta yanke hukuncin ne a ranar 22 ga watan Afrilu, 2024, kuma aka rabawa manema labarai takardar hukuncin a ranar Lahadi a Abuja.
