Majalisar Dattawa Ta Gano Shigowar Wani Gurbataccen Man Fetur Mai Hatsari A Najeriya

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa mjalisar Dattawan Najeriya ta ankarar da ‘yan ?asar cewa an shigo da wani nau’i na gur?ataccen man fetur da kuma dizel cikin ?asar.

Da yake gabatar da wani ?udiri a ranar Laraba, Sanata Asuquo Ekpeyong ya ce a ranar 16 ga watan Yunin 2024 wani rahoto ya nuna cewa wasu jiragen dakon kaya 12 sun kai tan 660 na man dizel zuwa birnin Lome na Togo, inda daga nan aka rarraba su zuwa ?asashen Afirka ta Yamma musamman Najeriya.

A cewarsa, ingancin man bai kai na wanda aka saba amfani da shi a Najeriya ba.
Ya kuma ce duk da hukumar kula da ha?owa da kuma cinikin man fetur ta NMDPRA ta sauya dokokin nau’in man da ake amfani da shi kamar yadda sabuwar dokar man fetur ta tanada, ba ta iya saka ido kan amfani da man a fa?in ?asar.

Daga baya Majalisar ta kafa kwamatin gaggawa don bincika man da ake shigowa da shi, wanda suka ce yana da ha?ari.

Related posts

Leave a Comment