An Tsame Manoma Da Kananan ‘Yan Kasuwa Daga Harajin Cinikayya A Najeriya

images 2024 03 14T070645.613

Gwamnatin Najeriya ta tsame manoma da ?ananan ?an kasuwa da masu kamfanoni daga biyan haraji na cinikayya.

Shugaban kwamitin shugaban ?asa kan yi wa haraji garambawul a Najeriya, Taiwo Oyedele ne ya sanar da matakin a shafinsa na X.

Ya ce muhimman sauye-sauyen da aka yi za su magance matsalolin da aka gano da kuma sanya masu ?ananan sana’oi cikin wa?anda aka tsame daga biyan harajin cinikayya, tsame masu kamfanoni da masu sarrafa kayayyaki kamar manoma: matakan da za su magance kauce wa biyan haraji.

Ya ce an bijiro da tsarin harajin a Najeriya a 1977.
An tsara shi ne domin bai wa gwamnati damar samun ku?a?en shiga a kai a kai tare da zama wata dama ta magance kauce wa biyan haraji, in ji kwararren kan haraji.

Related posts

Leave a Comment