Babu Batun Luwadi Da Madigo A Dokar Da Muka Sanya Wa Hannu – Fadar Shugaban Kasa

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa ministan ya?a labarai da wayar da kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ba za ta goyi bayan duk wani yun?uri na auren jinsi ko ?aure wa ‘yan luwa?i da masu ma?igo a Nijeriya ba.

Ministan ya fa?i haka ne a yayin da yake martani kan labarin da aka ya?a a ranar Alhamis cewa Gwamnatin Tarayya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da aka yi a ?asar Samoa, wadda za ta ba da dama a hukumance ga ‘yan luwa?i da masu ma?igo a Nijeriya.

A rahoton da wasu kafafen ya?a labarai suka buga, an ruwaito cewa yarjejeniyar ta ?unshi wasu tanade-tanade ne wa?anda ke bu?atar goyon bayan kare ha??in ‘yan luwa?i da masu ma?igo a matsayin shara?in samun tallafin ku?i da sauran taimako daga ?asashen da suka ci gaba.

Lamarin dai ya haifar da ce-ce-ku-ce, inda wasu malaman addini da masu rajin kare ha??in ?an’adam ke sukar gwamnati kan amincewa da yarjejeniyar da ta yi.

To amma a ?arin hasken da ya yi kan yarjejeniyar, Minista Idris ya ce ai Nijeriya tana da dokoki tun tuni wa?anda suka haramta auren jinsi ko tarayyar ‘yan luwa?i da masu ma?igo, kuma dokokin sun girmi wannan yarjejeniyar ta Samoa da ake ta ce-ce-ku-ce a kan ta.

Ya ce, “A ranar 28 ga Yuni, 2024 ne gwamnatin Nijeriya ta rattaba hannu kan yarjejeniyar Samoa ?in a sakatariyar ?ungiyar ?asashen Afirka, Karibbiyan da Pacific (OACPS) a birnin Brussels na ?asar Beljiyam.

“An fara tattaunawa kan yarjejeniyar tun a shekarar 2018, a lokacin taron Majalisar ?inkin Duniya karo na 73. ?aukacin ?asashe membobin Tarayyar Turai su 27 da ?asashe 47 daga cikin 79 na OACPS ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar a garin Apia da ke Tsibirin Samoa a ranar 15 ga Nuwamba, 2018.

“Nijeriya ta rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a ranar Juma’a, 28 ga Yuni, 2024. Hakan ya biyo bayan nazarin da ta yi tare da tuntu?ar Kwamitin Ministoci da Ma’aikatar Kasafin Ku?i da Tsare-tsaren Tattalin Arziki ta kafa tare da ha?in gwiwar Ma’aikatar Harkokin ?asashen Waje da Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya.

“An tabbatar da cewa babu ?aya daga cikin Tanade-tanade 103 na yarjejeniyar wa?anda suka sa?a wa Kundin Tsarin Mulki na 1999 wanda aka yi wa kwaskwarima ko dokokin Nijeriya, da sauran wasu dokoki.

“Bugu da ?ari, amincewar da Nijeriya ta yi yana ?unshe da sanarwa mai ?auke da kwanan wata 26 ga Yuni, 2024, inda ta fayyace fahimtar ta da kuma yanayin yarjejeniyar a ?ar?ashin ikon ta na cewa ba a amince da duk wani tanadi da ya sa?a wa dokokin Nijeriya ba.

“Yana da kyau a lura da cewa akwai dokar da aka kafa a Nijeriya game da dangantakar auren jinsi ?aya tun a cikin 2014.”

A ?arshe, ministan ya ce, “Ya zama wajibi a tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, kasancewar ta gwamnati mai bin ?a’ida, ba za ta shiga wata yarjejeniya ta ?asa da ?asa wadda za ta cutar da ?asa da ‘yan ?asar ta ba.

“Yarjejeniyar Samoa ba komai ba ce illa wani muhimmin tsarin doka na ha?in gwiwa tsakanin ?asashen ?ungiyar OACPS da Tarayyar Turai don inganta cigaba mai ?orewa, da ya?i da sauyin yanayi da illolin sa, da samar da damar zuba jari, da samar da ha?in gwiwa tsakanin ?asashe membobin OACPS a matakin ?asa da ?asa.”

Related posts

Leave a Comment