Bani Da Hannu A Zanga-zangar SARS – Tinubu

Jagoran jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya nisanta kansa daga zanga-zangar EndSARS da matasa suka shafe mako biyu suna yi a wasu jihohin ?asar.

Mai magana da yawun Tinubu, Tunde Rahman, ya fa?a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Asabar cewa ba daidai ba ne a ce mai gidan nasa ne ke ?aukar nauyin zanga-zangar, kamar yadda ake ya?awa.

Ya ce abu ne mai wuya Tinubu ya iya ?aukar nauyin zanga-zangar a duka jihohin da ake yi.

“Ba zai yiwu Asiwaju Tinubu ya ?auki nauyin zanga-zangar da ta toshe ?aya daga cikin hanyoyin shiga da fita daga Jihar Legas ba, wadda take ?aya daga hanyoyin samun ku?in shiga ga gwamnatin jihar,” a cewar sanarwar.

“Kazalika, ba zai yiwu ya ?auki nauyin zanga-zangar ba a jihohin da su kansu masu zanga-zangar ke adawa da shi.”

Haka nan sanarwar ta ce Tinubu ya aminta cewa ya kamata a rushe rundunar SARS sakamakon “lokaci mai tsawo da ta ?auka tana cin zarafin matasa da sauran ‘yan ?asa” kamar yadda masu zanga-zangar suka bu?ata.

Sai dai ya ce ya kamata a nemi hanyoyin lumana domin gabatar da bu?atu ga gwamnati.

Related posts

Leave a Comment