Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa hukumar ‘yan sandan farin kaya DSS ta tabbatar da gayyatar tsohon Gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari zuwa ofishinta.
Sai dai hukumar ba ta fa?i dalilin da ya sa ta gayyace shi ba, tana mai musanta “jita-jitar” da ake ya?awa cewa an tsare shi ne saboda ya ?i amsa wayar Shugaban ?asa Bola Tinubu.
A ranar Asabar ne wasu rahotanni da aka wallafa a shafukan intanet suka ce DSS ta kama tsohon gwamnan ne saboda ya ?i sauraron shugaban ?asar game da za?en shugaban Majalisar Dattawa da aka yi a watan da ya gabata.
DSS ta bayyana labarin a matsayin “na ?arya” kuma “abin dariya”.
“Abu ne maras amfani ko kuma na dariya….Wannan shi ake kira shashanci a rahoto. Yari ya san dalilin da ya sa aka gayyace shi,” a cewar sanarwar da DSS ta wallafa a shafinta na Twitter.
