Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Kungiyar masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar sun yi kira ga shugabancin jam’iyyar da ta tabbatar da ganin cewa magajin Gwamna Nasir El-Rufai ya kasance mai ilimi sosai kamar Gwamnan.
Sun ?ara da cewar yana da matukar muhimmanci ga jihar ta samu mutum mai ilimi kamar El-Rufai domin ci gaba da kyawawan manufofin gwamnan na raya ?asa.
Da yake jawabi a madadin kungiyar a wani taron manema labarai a Kaduna, tsohon babban mai ba Gwamna Nasir El-Rufai shawara ta musamman, Dr Usman Ahmed Danbaba, ya ce zagayen ‘shiyya ta ?aya zai samar da gwamna na gaba.
Ya kuma jadadda cewar yankin na da mutane masu tarin ilimi domin shiga neman takarar kujerar gwamna a karkashin jam’iyyar.
A cewarsa, yankin arewacin Kaduna bai amfana daga kowane babban mukamin siyasa ba tsawon shekaru bakwai da suka wuce a gwamnatin APC a jihar.
Ya ce sanatan, mambobin majalisar wakilai shida, 11 daga cikin 12 na yan majalisar dokokin jihar, 7 daga cikin 8 na shugabannin kananan hukumomi daga yankin duk yan APC ne.
Sai dai kuma ya ce babu gwamna, mataimakin gwamna, ministoci biyu, shugaban jam’iyyar, sakataren jam’iyyar, shugabar mata, shugaban matasa ko wakilin jihar a APC ta kasa da ya fito daga yankin.
“Mun yarda cewa ya kamata a saurara sannan a mutunta ra’ayoyinmu da matsayarmu a zaben fidda gwani na jam’iyyarmu mai zuwa. Musamman, tunda ya shafi zabin wanda zai gaji shugabanmu, Mallam El-Rufai.
“Abune da kowa ya sani cewa yankinmu shine inda APC ta fi karfi a jihar, jajircewarmu sun yi fice a dukkan zabukan baya na 2015 da 2019 da zabukan kananan hukumomi da aka yi a kwanaki.”
Kungiyar ta kuma kara da cewa suna bukatar dan takara da ya cancanta, mai tafiya da kowa kuma wanda ya san manufofi da tsare-tsare na gwamnatin Gwamna El-Eufai.
