Babban Bankin Kasa Ya Yi Karin Kudin Ruwa Sau Biyu A Wata Guda

IMG 20240228 WA0023

Babban Bankin Najeriya ya yi ?arin ku?in ruwa da kashi 2% karo na biyu kenan cikin wata ?aya, inda yanzu ya kai kashi 24.75, a cewar gwamnan bankin Olayemi Cardoso.

Shi ne karo na biyu da CBN ya yi ?arin a cikin wata daya, bayan ?ara kashi 4% a watan Fabrairu.

Shawarar babban bankin wanda shi ne ?ari mafi yawa a cikin kusan shekara biyu, na da nufin ta?aita samun ku?a?en jari da rage hauhawar farashi.

Hauhawar farashi a Najeriya yanzu ta kai kashi 31.7%, sanadin tsadar farashin abinci da na makamashi, tashin ku?in sufuri da kuma ta?ar?arewar tsaro a yankunan da ake samar da abinci.

Kayan abincin sun ha?ar da burodi da shinkafa da nama da nono da kayan marmari duka sun ninka farashinsu.

Najeriya mafi girman tattalin arzi?i a Afirka na fuskantar tsattsauran yanayin tattalin arzi?i, lamarin da ya ingiza mutane da dama cikin talauci.

Related posts

Leave a Comment