Labarin dake shigo mana daga Gusau babban birnin jihar Zamfara na bayyana cewar shugaban kwamitin sassanci da yan bindiga Alhaji Abdullahi Shinkafi ya koka kan yadda ake tafiyar hawainiya wurin bincike da hukunta yan bindiga dake addabar Jihar har da ma?wabta.
Ya yi wannan jawabin ne a ranar Talata bayan kwamitinsa ya gudanar da wani muhimmin taro da masu ruwa da tsaki kan harkar tsaro a jihar.
“Babban matsalar da muke samu shine jami’an tsaro da alkalai da lauyoyi da ke kare masu laifin, idan ka kama yan bindiga da AK-47 11, wane hujja ka ke jira? Ya kamata a aika shi wurin mahallacinsa. “Idan an kama dan bindiga dumu-dumu, yana kashe mutane kuma kana jiran bincike, mene ka ke bincikawa? Ka aika shi wurin mahallicinsa.”
Abdullahi Shinkafi, ya ce kwamitinsa ba zai sake sasanci da wani dan bindiga ba domin mafi yawancinsu ba da gaske suke ba. “A bangare na, kan batun tuban Turji na san ya rungumi zaman lafiya amma ba zan iya cewa ya tuba ba, sai ya mika wuya tare da dukkan bindigogi da makamansa, ya zo gidan gwamnati ya mika makamansa kamar yadda sauran tubabbun yan bindiga suka yi.
“Duk wani batun sasanci da yan bindiga, a cire ni daga ciki domin mafi yawancinsu ba da gaske suke yi ba, yaudaran mu suke, duk wani yarjejeniya da kuka yi da su, za su koma mummunar sana’arsu, mafi yawancin su.”
