Labarin dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewar Shugaban jam’iyyar APC na jihar Abdullahi Abbas ya sake ?aro wata magana da ake ganin za ta iya haifar da rikici a za?en dake tafe musanman na Gwamna a jihar Kano.
“Ko da tsiya ko da tsiya-tsiya, ko ana ha-maza ha-mata, ko me za a yi, ko me zai faru, ko mai tafanjama fanjam sai mun ci za?e,” in ji Abdullahi Abbas.
Shugaban jam’iyyar APC ?in, ya yi wa?annan kalamai ne a ranar Laraba yayin da suke ?addamar da kamfe ?in takarar gwamna a ?aramar Hukumar Gaya.
A? bayyane take ciyaman ?in yana sane da cewa kalaman da yake yi ba su dace ba amma duk da haka sai ya fa?a.
K?afin ya fara ?a?atun sai da ya ce: “…ina tabbatar muku cewa wannan alama ce ta cin za?e. Wannan karon, duk da cewa an ce na daina fa?a, ko da tsiya…”
B?BC ta nemi jin dalilinsa na yin wa?annan kalamai amma bai ?aga waya ba sannan kuma bai amsa sa?on tes da muka tura masa ba.
Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ne ya jagoranci taron, wanda ya samu halartar mataimakin gwamnan kuma ?an takarar APC, Nasiru Yusuf Gawuna, da abokin takararsa Murtala Garo, da Sanata Kabiru Ibrahim Gaya.
Kalaman nasa na zuwa ne a lokacin da hukumomi a cikin gida da ?asashen waje ke kira ga ‘yan siyasa da guji kalaman tayar da fitina.
