Ko A Masallacin Ka’aba Ba Zan Nemi Gafarar Masari Ba – Mahdi Shehu


Shugaban Kamfanin Dialogue Group, Shehu Mahdi, ya ?aryata wasi?ar neman afuwar Gwamnan Katsina, Bello Masari, kan batun ya?a bayanan bogi a kansa da aka ce ya aika wa gwamnan.

A ranar Alhamis, 23 ga Satumban 2021 aka ga bayyanar wata wasi?a ta neman yafiya zuwa ga Gwamna Masari da ma al’ummar jihar wadda aka ce Mahdi ne ya rubuta tare da aikawa da ita ga gwamnan.

Sai dai, cikin wani sa?on bidiyo da ya kara?e kafofin sadarwa mai tsawon minti 10, an ga Shehu Mahdi na bayani cikin harshen Ingilishi inda ya ?aryata wasi?ar, yana mai cewa ko ka?an ba shi ya rubuta wasi?ar ba. Ya ce wannan ba komai ba ne face aikin wasu da ba su manufa balle buri a rayuwa.

A cewar Mahdi, da farko bai so cewa komai a kan wasi?ar ba, amma domin wayar da kan ?imbin masoyansa shi ya sa ya fito ya ?aryata wasi?ar.

Ya ce hatta takardar da aka rubuta wasi?ar a kai ba ta kamfaninsa ba ce kamar yadda aka yi i?irari, balle kuma samfurin sa hannun da ke cikin wasi?ar, wannan ma ya ce ba sa hannunsa ba ne

A cewar Mahdi, shi bai ga yadda za a yi ya rubuta irin wannan wasi?ar ba sanin cewar sun shiga kotu kan batutuwan da wasi?ar ta ?unsa.

Haka nan ya ce, shi mutum ne wanda muddin ya san cewa yana kan hanyar da ta ce kan wani al’amari, to, ko ta halin ?a?a zai ci gaba da gwagwarmaya ba tsoro ba ja da baya har sai ya cimma ?udirinsa. Ya ce shi ba wawa ba ne da zai fito ya bai wa Masari ko wani jami’in gwamnati ha?uri, yana mai cewa matsayinsa ya zarce haka.

Ya ci gaba cewa, ya gamsu kan cewa duk wa?anda suka yi masa farin sani, ya tabbata ba za su ta?a yarda da wancan wasi?ar bogin da aka fitar da sunansa ba.

Mahdi ya ?ara da cewa, shi fa a halin da ake ciki, “Da a ce zan ha?u da Bello Masari, ko El-Mansuk, ko Mustapha Inuwa Masallacin Makka, ko Madina, ko kuma Baitul Mu?addas don aikin Hajji ko makamancin haka, sanan dukkansu ko ?ayansu ya yi mini sallama, ba zan amsa sallamar ba.

“Haka ma ko hannu suka mi?o mini don yin musabaha, ba zan kar?a ba saboda ban yarda da su ba.”

Ya ci gaba da cewa, “‘Yar tsamar da ke tsakanina da su ta har abada ce. Kuma shekaruna sun wuce na bada ha?uri a inda bada ha?urin bai da wani amfani. Babu wanda ya isa ya yi mini wata barazana a wannan shekarun nawa.”

Mahdi ya kammala sa?on nasa da ro?on Allah kan duk wanda ke da hannu cikin wannan wasi?ar bogin, Allah ya jarabce shi da masifa kan masifa, ba?in ciki kan ba?in ciki, cuta kan cuta, hasara kan hasara da sauransu.

Related posts

Leave a Comment