Ba Mu Janye Tuhumar Da Muke Yi Wa Tukur Mamu Ba – DSS

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta musanta rahoton da ke yawo cewa ta janye ?arar data shigar kan Tukur Mamu, tsohon mai shiga tsakani da ‘yan ta’adda.

Wani rahoton da ake ya?awa ya yi ikirarin cewa hukumar ta janye ?arar da ta shigar a babbar Kotun tarayya mai zama a Abuja, inda ta samu sahalewar tsare shi na kwana 60.

Rahoton ya nuna Lauyan DSS, A. M Danlami ya shaida wa Mai shari’a Nkeonye Maha, jim ka?an bayan kiran ?arar, cewa hukumar ta jingine shari’ar.

Amma a wata hira da jaridar Daily Trust ranar Alhamis da daddare, mai magana da yawun hukumar DSS, Peter Afunanya, ya bayyana rahoton da, “Karya mara tushe.”

Mista Afunanya ya jaddada cewa DSS ba ta janye ko tuhuma ?aya da take wa Tukur Mamu ba, inda ya bayyana cewa lamarin wani batu ne da za’a cigaba da shi.

Idan baku manta ba a ranar 6 ga watan Satumba, 2022, Jami’an tsaro suka kama Mamu a Cairo, babban birnin ?asar Masar lokacin yana tare da iyalansa.

Mamu, fitaccen ?an jarida a Kaduna kuma makusancin Shahararren Malamin Nan, Sheikh Ahmad Gumi, shi ya shiga tsakanin gwamnatin tarayya da ‘yan ta’addan da suka yi garkuwa da Fasinjojin jirgin ?asan Abuja-Kaduna.

Related posts

Leave a Comment