Kisan Gillar Jos: Pantami Ya Wakilci Buhari Wajen Yi Wa Bauchi Ta’aziya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari Ya wakilta Malam Isa Ali Ibrahim Pantami ya jagoranci zuwa ta’aziyya ga Shaykh Dahiru Usman Bauchi bisa ga kisan gilla da akayi wa dalibansa. Kuma a tabbatar masa da Gwamnati ta bada umurni a binciki masu laifi, a musu hukunci kamar yadda doka ta tsara.

Malam Pantami ya gana da Shaykh Dahiru Bauchi, sannan Ya isar da ta’aziyya ga Shaykh. Sannan kuma Shugaban Kasa zai gana da Shaykh Dahiru in Allah Ya yarda bayan kammala isolation na tafiyar da yayi, a cikin wannan sati.

Muna adduar Allah Ya jikan bayinsa da suka riga mu gidan gaskiya. Ya gafarta masu, sannan Ya sa Aljannah ce makomarsu da mu baki daya. Kuma Allah Ya kawo karshen tashin hankali a Nijeriya, Ya kuma tona asirin masu tayarwa.

Related posts

Leave a Comment