Babbar Magana: Gwamnoni Sun Maka Buhari Gaban Kuliya

Gwamnonin Najeriya su 36 sun maka Gwamnantin Shugaba Muhammadu Buhari Kotun Koli, su na zargin Buhari ya karkatar da ku?a?en da aka ?wato daga ?arayin gwamnati har naira tiriliyan 1.8, sai kuma kadarorin da aka ?waro na naira biliyan 450.

Gwamnonin dai sun yi zargin cewa Gwamnatin Buhari ta dan?ara ku?a?en cikin Asusun Tara Ku?a?en Shigar Gwamnatin Tarayya, wato ‘Consolidated Revenue Account’ (CRA), wanda yin hakan kuwa babban laifi ne, kuma take Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ne ?arara.

Gwamnonin 36 sun shaida wa Kotun ?oli cewa, dokar tsarin mulkin Najeriya cewa ta yi a tara ku?a?en da kadarorin a ?ar?ashin Asusun Tara Ku?a?e pDa Kadarorin Sata Na Gwamnatin Tarayya, wato ‘FGN Assets Recovery Account’ (FGNARA) da ke a Babban Bankin Najeriya.

A cikin kwafen ?arar da su ka shigar, sun ce abin da gwamnatin Buhari ya yi ya karya dokar ?asar nan ?uru-?uru.

“Asusun Gwamnantin Tarayya nan ne ya wajaba a tara ku?a?en a cikin Asusun Tara Ku?a?en Sata, Babban Bankin Najeriya. Saboda shi ne asusun da doka ta yarda a ri?a raba ku?a?en da ke ciki tsakanin Tarayya, Jihohi da ?ananan Hukumomi.

“Shi kuma Asusun Tara Ku?a?en Shigar Gwamnatin Tarayya na CRA, asusu ne kawai na tara wa gwamnatin tarayya ku?a?en shiga da su ka ha?a da ku?a?en harajin da lasisin da gwamnatin tarayya ke kar?a, ku?a?en harajin filaye da gonaki, ku?a?en ruwa da gwamnatin tarayya ta kar?a daga wa?ansu hannayen jarin ta da sauran su.”

Babban Daraktan ?ungiyar Gwamnonin Najeriya 36 (NGF), Asishanu Okauru ne ya bayyana haka a cikin kwafen takardar da ya maka Gwamnantin Tarayya ?ara, a madadin ?ungiyar gwamnonin.

“Abin da Gwamnatin Buhari ta yi ya sa?a wa Sashe na 162 (1), 162 (10) da kuma Sashe na 80 na Dokar Ku?a?e ta 1958.” Inji Okauru.

Ya ce dukkan wa?annan sassa sun nuna cewa a Asusun Gwamnantin Tarayya za a ri?a ajiye dukkan ku?a?en da aka kar?o daga ?arayin gwamnati, a cikin Asusun Bai ?aya Na Gwamnatin Siriya.

Gwamnonin Najeriya 30 Sun Nemi Kotun ?oli Ta Tilasta Wa Shugaba Buhari:

1. Ya maida naira tiriliyan 1.8 daga Asusun CRA da kuma Kadarorin naira biliyan 450 duk zuwa cikin Asusun FGNARA da ke cikin Baban Bankin Najeriya, CBN.

2. Sun bu?aci Kotun ?oli ta tilasta wa Shugaba Buhari bayyana dalla-dallar adadin ku?a?en da aka ?wato a hannun ?arayin gwamnati, wa?anda bai saka a Asusun Gwamnantin Tarayya ba.

3. Kotun ?oli ta tilasta wa Hukumar Raba Ku?a?en Gwamnatin Tarayya (RMFAC), ta tsara yadda za a ri?a raba ku?a?en Gwamnanti tsakanin Tarayya da Jihohi da Kananan Hukumomi.

Babban Lauya kuma fitaccen nan Femi Falana ke jagorantar lauyoyin Gwamnonin Jihohi su 36.

Related posts

Leave a Comment