Ketare: ECOWAS Ta Yi Tir Da Juyin Mulkin Burkina Faso

?ungiyar ha?aka tattalin arzikin ?asashen Afirka ta Yamma, Ecowas, ta yi wadarai da juyin mulkin da sojoji suka yi a Burkina Faso, tana mai bayyana shi da “koma-baya” bayan ci gaban da aka samu.

“Ecowas na jaddada rashin amincewarta da ?wace mulki ba ta hanyar da kundin tsarin mulki ya tanada ba,” a cewar sanarwar da ta fitar.

Ta ?ara da cewa “muna kira da a yi gaggawar komawa kan yarjejeniyar da aka cimma ta mayar da mulki ga farar hula a ranar 1 ga watan Yulin 2024”.

?ungiyar mai hedikwata a Abuja ta garga?i “duk wani mutum ko tawaga wa?anda aikinsu zai iya kawo tsaiko wajen mayar da mulki ga farar hula ko kuma tayar da hankali a Burkina Faso”.

Ita ma takwararta ta AU ta yi Allah-wadai da juyin mulkin, wanda Kaftin Ibrahim Traore ya jagoranta inda ya ham?arar da Kanar Damiba wanda ya hau mulki a watan Janairun da ya wuce ta hanyar juyin mulki.

Related posts

Leave a Comment