Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kebbi na bayyana cewar a ranar Litinin ne ragowar ?aliban sakandiren Yawuri dake jihar suka cika wata 11 a hannun ‘yan bindiga.
A tsakiyar watan Yunin bara ne ‘yan bindigar suka auka Kwalejin Tarayya ta Yawuri, kuma suka yi awon gaba da gwamman ?alibai.
Sai dai kuma ‘yan fashin da suka yi garkuwa da ?aliban sun saki dukkan mazan da ke hannunsu amma suka ci gaba da ri?e wasu ‘yan mata.
Ranar Lahadi da yamma iyayen ?aliban sun gudanar da taro game da wannan lamari, kuma ?aya daga cikinsu ya fada wa BBC cewa har yanzu basu debe tsammanin sake haduwa da ya’yan nasu ba.
Cikin yanayi na damuwa da takaici, daya daga cikin iyayen yace ”ana rana ana hunturu ana ruwa ana zafi yarannan na hannun barayi saboda Allah.”
Mahaifin ya kara da cewa suna zargin cewa babu abin da gwamnatin Jihar Kebbi ke yi don ganin ta kwato musu ‘ya’yansu hannun yan bindigar.
Da ya ke magana kan gwamna Atiku Bagudu mahaifin ya ce ”shi Atiku Bagudu da ya yi alkawarin cewa zai kubutar da yaran gaba daya idan mun tuntube shi ta waya ma baya daukar wayarmu.”
”Ainihin wanda ya hada mu dashi wanda dashi ake zuwa daji lokacin ya nuna mana cewa ba batunmu yake ba, kuma idan ya kira shi ga waya ma baya dauka.” In ji mahaifin.
Akan haka ya ce suka sake zama da wasu iyaye, don su sake lale, kuma su samu tabbaci daga gwamnati cewa ta gaza don su daina dogara gare ta.
