Kotu Ta Mayar Wa Mahadi Aliyu Mukamin Mataimakin Gwamnan Zamfara

Wata babbar kotun tarayya mai zamanta a birnin tarayya Abuja, ta mayar da Mahadi Aliyu Gusau a matsayin mataimakin gwamnan jihar Zamfara.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa Gusau da PDP sun shigar da ?ara ne kan hanyar da majalisar dokokin jihar ta bi ta tsige shi daga mu?aminsa a watan Fabrairun 2022.

Da yake zartar da hukuncinsa a ranar Laraba, mai sharia Inyang Ekwo ya bayyana cewa kwamitin bincike da tsohon gwamnan jihar Bello Matawalle ya kafa ya sa?a doka.

Al?alin ya bayar da umarnin mayar da Mahadi mu?amin mataimakin gwamna tun daga ranar da ya shigar da ?ara a watan Yulin 2021. Ya kuma kawar da dukkanin matakai da hanyoyin da aka bi wajen tsige mataimakin gwamnan a lokacin da ?arar ta ke a gaban kotun.

“A dalilin hakan an bayar da umarnin mayar da wanda ya shigar da ?ara (Mahadi Aliyu Mohammed) kan mu?aminsa na mataimakin gwamnan jihar Zamfara, tun daga ranar 8 ga watan Yulin 2021 lokacin da aka fara sauraron wannan ?arar.” A cewar al?alin. “An kuma bayar da umarnin jingine duk wani hukunci da wa?anda ake ?arar suka ?auka wajen tsige mataimakin gwamnan jihar Zamfara, a lokacin da wannan ?arar ta ke a gaban kotun nan.

Related posts

Leave a Comment