2023: APC Ta Musanta Sauya Jadawalin Shirye Shiryen Zabe

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Jam’iyyar APC ta musanta cewa ta sauya jadawalin shirye-shiryen za?en 2023

Jam’iyyar APC ta bu?aci jama’a da su yi watsi da ra?e-ra?in da ake ta ya?a wa cewa ta sauya jadawalinta shirye-shiryen tunkarar babban za?en 2023.

Felix Morka, Sakataren Ya?a Labarai na Jam’iyyar, a cikin wata sanarwa da ya fitar a daren Litinin, ya ce rahoton sauya za?ukan fitar da gwani na jam’iyyar na bogi ne, ya kamata a yi watsi da shi.

“An ja hankalinmu kan wani labari da a ke ya?a wa cewa jam’iyar mu ta sauya jadawalin ayyuka da tsare-tsaren zaben 2023 a shafukan sada zumunta.

“Ya kamata a yi watsi da labarin a matsayin labaran karya,” in ji shi.

Ya kara da cewa jadawalin jam’iyyar da tsare-tsaren ayyukan shiga zaben 2023 ya kasance kamar yadda aka buga a baya.

Ya sake bayyana jadawalin da aka amince da shi kamar haka.

Za?en Gwamna- Juma’a, Mayu 20, 2022.

Za?en Majalisar Dokoki ta Jiha – Lahadi, 22 ga Mayu, 2022.

Za?en Majalisar Wakilai – Talata, Mayu 24, 2022.

Za?en Majalisar Dattawa – Laraba, Mayu 25, 2022.

Za?en Shugaban kasa – Litinin, Mayu 30th zuwa Yuni 1st, 2022.

Related posts

Leave a Comment