Labarin dake shigo mana daga jihar Katsina na bayyana cewar Dakarun ‘Yan Sandan sun kashe ‘yan bindiga da dama a Jihar bayan wani samame da suka kai musu da tsakar dare a ranar Alhamis.
A cewar sanarwar da kakakin ‘yan sandan Katsina SP Gambo Isah, lamarin ya faru da misalin ?arfe 1:00 na dare bayan an yi wa jami’an tsaron kiran neman ?auki a ?aramar Hukumar Kurfi.
Ya ?ara da cewa da jin haka ne dakarunsu suka isa wurin kuma suka far wa maharan.
