Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya yi garga?in cewa aikin gwamnati ba juji bane ga miliyoyin masu neman aiki a fa?in tarayyar ?asar.
Shugaban ya yi garga?in ne a ranar Juma’a yayin da yake kar?ar ba?uncin Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya Folashade Yemi-Esan a fadarsa da ke Abuja.
Ya ce “kamata ya yi aikin gwamnati ya zama wurin da zai dinga ha?o kan mafiya ?warewa don magance matsalolin da ke addabar ?asa”.
Yayin ziyarar, an gabatar wa shugaban rahoton binciken kwamatin Orosanye kan aikin gwamnati, wanda Buhari ya umarci a fara duba shi nan take “don yi wa aikin gwamnati kwaskwarima” a Najeriya.
Al?aluman da Hukumar ?ididdiga ta ?asa ta fitar a wata ukun farko na shekarar 2021 ya nuna cewa rashin aikin yi ya kai kashi 33 cikin 100 a Najeriya.
