Buhari Bai Da Masaniya Kan Badakalar Emefiele – Fadar Shugaban Kasa

Fadar shugaban kasa ta ce yawancin ku?a?en da aka fitar daga Babban bankin ?asar (CBN) ?ar?ashin shugabancin Godwin Emefiele, an fitar da su ne ba tare da sa hannun tsohon shugaban ?asa Muhammadu Buhari ba.

Ajuri Ngelale, mashawarci na musamman ga shugaban ?asa Bola Tinubu kan harkokin ya?a labarai da wayar da kan jama’a ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi a shirin With Chude na Chude Jideonwo wanda aka watsa a gidan talabijin na Channels.

Ngelale ya ce dole ne gwamnatin da ta gabata ta ?auki alhakin wasu abubuwan da suka faru a babban bankin ?ar?ashin jagorancin Emefiele.

Ngelale ya jaddada cewa, yayin da Buhari ya samu nasarori a wasu fannonin samar da ababen more rayuwa, rashin sanya ido kan al’amuran Babban bankin ya taimaka wajen ta?ar?arewar tattalin arzi?in ?asar.

Duk da cewa ya amince cewar Bola Tinubu ya bai wa gwamnati tsohon shugaban ?asa Muhammadu Buhari goyon baya, Ngelale ya ce a yanzu Tinubu na ?o?arin ganin ya magance matsalolin da suka haifar da ta?ar?arewar tattalin arzikin kasar da ta faru a zamanin gwamnatin Buhari.

Related posts

Leave a Comment