Katsina: ‘Yan Bindiga Sun Sace Amarya A Daren Amarci

Rahotanni daga jihar Katsina na bayyana cewa wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da kanwar mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar, Shehu Dalhatu Tafoki.

An sace Asama’u Dalhatu ana tsaka da shirye-shiryen soma bikinta, a cewar ?an majalisar.

?an bindigar sun kai hari ne kauyen Tafoki da ke karamar hukumar Faskarin Katsina tare da sace Amaryar.

A lokacin tabbatar da faruwar lamarin, ?an majalisar ya shaida wa jaridar Daily Trust cew an sace kanwar tasa da sanyin safiyar Lahadin.

Ya kara da cewa har yanzu ‘yan bindigar ba su tuntube su ba domin neman kudin fansa.

Related posts

Leave a Comment